Jami'an tsaro a tashar jiragen sama na birnin Keflavik, a kasar Iceland, sun haramta ma Mr. Ryan Carney Williams, shiga jirgin sama, bayan ya sayi tikitin tafiya bisa dalilin cewar ya dibga duk kayan sawarsa a jiki domin kada ya biya kudin kaya.
Mr. Ryan, yana kan hanyar sa ta zuwa birnin Londan, bayan ya sanya dukkan kayan da yake dauke dasu a jikin sa ganin cewar akwatin sa bazai dauki dukkan kayan ba.
Ryan wanda ake kira Ryan Hawaii, yayi amfani da shafin sada zumunta na Twitter inda ya bayyana abin da ya faru da shi har yana tambaya ko wariyar launin fata ce ta sa aka hana shi shiga cikin jirgin.
Amma kamfanin jirgin ya musanta abinda Ryan ya fada, inda ya bayyana cewa an hana shi shiga ne saboda rashin kunyar da yayi a lokacin, kuma suka ce ya bar wajen amma bai bi ummurnin ma'aikatan ba, dalilin da yasa aka kira mashi jami’an tsaro kenan.
A wani sakon da ya kara rubutawa a shafin twitter, Ryan ya ce an kwala mashi kulki, kuma aka tilasta shi ya kwanta a kasa daga bisani kuma ‘yan sanda suka tafi dashi.
Bayan ya ba ‘yan sanda bayani, sun sake shi domin ya koma filin jirgin don ya hau wani jirgin da ya biya na kamfanin Easy Jet, amma shima sai aka hanashi shiga.
Mai magana da yawum kamfanin Easy Jet, ya ce “hukuncin da aka dauka na hana shi shiga jirgin, ba an dauke shi ne akan saboda launin fatar sa ba. Ya kara da cewar, bama lamuntar tsoratarwa, barazana da kuma rashin da’a daga fasinjoji kuma a kowanne lokaci hakan ta faru zamu dauki mataki.”