Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Faransa Ya Kirkiri Keke Na Farko A Duniya Mai Amfani Da Hydrogen


Kamfanin kasar Faransa na farko a duniya da ya fara kirkirar Keke mai amfani da sinadarin iskar Hydrogen, don saukaka sufuri ga ma’aikata ko jama’ar kasar.

Kamfanin ‘Pragma Industries’ dake da matsugunni a birnin Biarritz, kamfanin tare da hadin gwiwar gwamatin kasar sun kirkiri kekunan wadanda sojojin kasar suka fara amfani da irin shi, ya zuwa yanzu dai an sayar da adadin kekunan 60 ga karamar hukuma birnin Faris.

Adadin kudin keken na kaiwa yuro 7,500 kimanin naira milliyan uku, jama’a dai na kuka dangane da tsadar keken, mahukunta a kamfanin na kokarin rage kudin zuwa yuro 5,000.

A cewar shugaban kamfanin Mr. Pierre Forte, “Duk da cewar wasu kamfanoni da dama sun kirkiri kekuna masu amfani da wuta, amma babu wanda ya kirkiri mai amfani da isakar hydrogen sai mu.”

Keken na tafiyar kimanin kilomita 100 akan gwangwani biyu na iskar hydrogen kafin ya kare, wanda idan aka yi la’akari da sauran kekuna masu amfani da batiri za’a ga cewar yafi saukin amfani.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG