Kamfanin Apple Ya Bunkasa Tattalin Arzikin Kasar Taiwan

Yadda ake samun karuwar kera wayoyin hannu, kamfanin Apple, ya taimaka matuka wajen karuwar bunkasar tattalin arzikin kasar Taiwan, kawo yanzu kasar na kara zama wata matattarar cinikayyar kimiyya da fasaha.

Kamfanin Apple, ya samu kari a kudin shiga wanda ya kai kashi 5.7% fiye da kason shekarar 2016. Sabuwar wayar iPhone X, ta taimaka wajen karuwar kudin shiga da kimanin milliyan $383M.

Ana sa ran idan Allah, ya kai rai shekarar 2018, za’a kara samun yawaitar sayen wayar Apple baki daya, musamman iPhone X, hakan zai kara sa kasar ta Taiwan samun karin kudin shiga.

Daya daga cikin kamfanonin dake kera wata na’urar waya Faxconn, na kasar ta Taiwan, sunyi fice a duniya wajen kera na’urorin cikin rahusa. Kamfanin na Apple, zai maida hankali wajen yunkurin samar da kayan su daga kasar ta Taiwan.

Hakan kuwa ya biyo bayan ganin yadda yake samun saukin kera kayan shi, da kokarin baza su a kasuwannin duniya, kana da samun riba mai yawa.