Kawo Yanzu Na Yaye Sama Da Dalibai Dari Biyu-Inji Maryam Lawal Gwadabe

Maryam Lawal Gwadabe

Maryam Lawal Gwadabe - shugabar makarantar ' blue Sapphire E- Solution ICT and Business school', wato makarantar kimiyya da fasaha da harkar kasuwaci , cibiya ce da ke koyarda da daburun kasuwanci amma a kimiyance.

Malamar ta bayyana cewa kawo yanzu makarantarta ta yaye kimanin mata dari biyu wadanda suka kammala duk horaswa da daukar darussan da suka kamata su koya.

Maryam Gwadabe ta ce ta fara karatun kimiyya da fasaha ne bayan iyayenta sun bukaci ta karanci Biochemestry, ita kuma ba abinda ranta ke so bane a lokacin, dan haka ba ta samu makin da ya dace ba wanda zi bata damar shiga jami’a sai ta fara karatun computer a wata makaranta inda ta sami labarin suna tura dalibansu kasashen waje domin karo karatu.

Bayan kammala karunne ta ga maimakon ta fara neman aiki me zai hana ta fara tata sana’ar da zata koya wa matasa ilimin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da ilimin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da ilimin a kasuwanci!.

Your browser doesn’t support HTML5

Kawo Yanzu Na Yaye Sama Da Dalibai Dari Biyu-Inji Maryam Lawal Gwadabe