Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Ginawa Marasa Gahihu Gidaje 90 Da Kudin Aure


India Modi
India Modi

Wani attajirin dan kasuwar, a kasar Indiya, Ajay Munot, ya ginawa marasa galihu gidaje 90, a cikin kudade, da ya ware domin bikin auren ‘yarsa.

Ya ce a maimakon ya kashe duk wadannan kudade a bikin ‘yar tashi, bayan akwai mutane da dama a yankin Aurangabad, da ya fito dake bukatar muhalli shi yasa ya sake shawara kan kudaden da za’a kashi domin mabukata suma su dara.

Ajay Munot, ya kara da cewa ya yake abubuwa dama da shi aginisa basu da amfani shi yasa aka samu aiwatar da gina gidaje 90, ga marasa shi.

Ya ci gaba da cewa wannan wani sabon babi ne, ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shuni da suma su kwaikwayi irin wannan abinda taimakon domin agazawa mabukata, domin a cewarsa ya zama wajibi masu arziki su taimakawa na kasa dasu.

Ita kuwa amaryar ta bayyana farin cikinta ga wanna hangen nesa da mahaifinta yayi na ginawa mabukata gidaje tace ta dauki wannan tafkar dukwishin aure daga mahaifinta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG