Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Mai Shekaru 24 Ya Kashe Maihaifinsa


FILE - Three men walk in handcuffs after being arrested as organizers of an opposition demonstration, which was dispersed by police firing in the air, in Jenda, Burundi, June 12, 2015.
FILE - Three men walk in handcuffs after being arrested as organizers of an opposition demonstration, which was dispersed by police firing in the air, in Jenda, Burundi, June 12, 2015.

Wani matashi Babalola Rotimi, mai shekaru ashirin da hudu ya shigar hannun ‘yan Sanda, a bisa zargin sa da akeyi na kashe mahaifinsa a gidansa dake unguwar Magodo, a birnin Legas.

Jaridar Punch, ta ruwaito cewa matashi wanda aka dawo dashi gida daga kasar Ireland, yana zaune tare da iyayensa ne a unguwar Magodo.

Ranar lahadi 4, ga watan Disamba, ne wanda ake zargin ya kashe maihaifinsa mai shekaru hamsin da tara, da wuka, kuma ya dabawa mahaifiyarsa itama wuka, dai dai lokacin da ta leko bayan da ta ji hayaniya.

Wasu mutanen unguwar ne suka damke shi daga bisani suka mika shi ga hukumar ‘yan Sanda, jaridar tace da yake maida wa ‘yan Sanda ba’asi akan abinda ya faru, yace mahaifinsa ya yawaita cewar zai yi maganin shi.

Ya kuma kara da cewa shi baya jindadin zama da mahaifinsa, kuma ya kasa jure kalamansa gareshi saboda haka sai ya yanke shawarar ya kashe a wannan ranar.

Bayan da Babalola Rotimi, ya kashe mahaifinsa sai ya dauki katin bankinsa ya kuma nufin gidan man mahaifinsa inda ya nemi mai kula da gidan man da ya bashi kudi.

XS
SM
MD
LG