Shirin Samawa Matasa Dubu 200 Ayyukan Yi

N-Power Social Investment Programme

Gwamnatin Tarraiyyar Najeriya ta fara daukan matasa aiki Kamar yadda ta yi alkawali. Amma yunkurin ya samu cikas a jihohi da dama a shiyar Arewa mussamman a Jihar Neja, da Borno, da Adamawa, da jihar Katsina, da jihar Kano, da Kebi da jihar Zamfara. Yaya lamarin yake a yankunanku?

Ana iya aiko mana da sakon amsar wannan tambaya, ko kuma duk ra'ayoyinku kan abinda suka shafi matasa ta email zuwa ga Dandalinvoa@voanews.com

Ana iya ziyartar shafinmu na WhatsApp mai lambar waya +12025775834, "Dandalin VOA Hausa Group" ta yadda zaku rika aiko mana da sakonnin muryoyinku cikin sauki.