Masu Kutsen Satar Bayanai Na Cigaba Da Auna Manyan Sunaye

Har yanzu dai masu kutse na ci gaba da auna manyan sunaye a fannin fasaha, inda a wannan karon suka yiwa shugaban kamfanin Twitter Jack Dorsey kutse a shafinsa.

Kungiyar masu kutsen dake kiran kanta da suna OurMine, itace ta dauki alhakin wannan kutse da aka kaiwa shugaban Twitter. Baya ga haka, kungiyarce ke da alhakin yiwa shugaban Facebook Mark Zuckerberg da shugaban Google Sundar Pichai kutse a baya bayan nan.

Masu kutsen dai sun kafe wata sanarwa dake cewa, “Muna gwadon karfin tsaronka” wannan sanarwa ta zamanto iri ‘daya ce da wadda aka rubutawa sauran mutanen da akayiwa kutsen.

A cewar gidan jaridar Guardian, masu kutsen dai sun shiga cikin shafin Twitter ne yayinda suka biyo ta hanyar sadarwa ta Vine, wadda take mallakar kamfanin Twitter.

Cikin watan da ya gabata dai Twitter ta rufe wasu shafunan mutane bayan da aka kwarmata bayanan shiga shafukan.