Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yi Jana'izar Muhammad Ali Ranar Juma'a Idan Allah Ya Kaimu


Rahotanni sun bayyana cewa iyalan marigayi Muhammad Ali zakaran damben boxing na duniya sun bada sanarwar cewa za a yi jana’izar sa a ranar juma’a idan Allah ya kaimu a birnin Louisville na Jihar Kentucky a nan kasar Amurka inda aka haife shi.

Ana sa ran jama’a da dama harda tsohon shugaban kasar Amurka wato Bill Clinton da sauran masoyansa zasu halarci jana’izar wadda a cewar rahotannin za’a gudanar kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Muhammad Ali shahararren dan damben Boxing na duniya ya rasu yana da shekaru 74 a duniya, kum ya yi suna wajan sana’r sa wadda ya kafa tarihi da ita a duniya.

A cigaba da kasancewa da mu domin samun rahotanni akan da dumi dumin su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG