Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Malam Aminu Daurawa Akan Auren Zawarawa


Da farko malamin ya fara da sallama, sa'annan ya bayyana abin da ake nufi da auren zawarawa da kuma matakai uku na yanayin da ake kira zawarawa da kuma irin dalilan da kan yi sanadiyyar samun makoma cikin irin wannan yanayi.

Malam Aminu Daurawa dai yana daya daga cikin jigajigan hukumar hisba dake jahar Kano, kuma daya daga cikin wadanda suke da hannu wajan jagoranci da kuma tabbatar da yin komi ta hanyar da ta kamata domin a cewar sa, jama'a da dama sun dauki abin tamkar sana'a.

Malamin ya yi karin bayanin cewa da farko sun fuskanci wasu 'yan matsaloli amma daga karshe sun gano dabarar shawo kan lamarin kuma a cewar sa hakan ya taimaka kwarai wajan kara inganta lamarin da kawata shi.

Kwamandan ya kara da cewa a yanzu haka, hukumar ta aurar da sama da zawarawa dubu biyar kuma daga lokacin kawo yanzu an sami karuwa kusan yara dari tara duk ta wannan hanya.

Daga karshe ya yi bayanin yadda suke kokarin bukasa shirin domin a cewar sa yanzu haka suna da kusan mata zawarawa dari biyar da kusam maza dari hudu dake jiran nasu lokacin, kuma ba gwamnati kadai ba hatta wasu kungiyoyi da masu hannu da shuni kan taimaka wajan biyan kayan dakin ma'auratan da kuma sadaki.

Ga cikakken bayanin nasa a nan.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG