Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Kece Raini Tsakanin Arsenal Da Leicester City


A cigaba da wasannin Laliga da akeyi na shekarar 2016/17 a matakin mako na talatin da hudu jiya kungiyar kwallon kafa ta Sporting Gijon, tayi kunnen doki 1-1 tsakainta da Espanyol, Granada bata ji da dadiba a hannun Malaga daci 2-0 a gidanta, Atletico Madrid, ta sha kashi da kwallo 1-0 a hannun Villarreal.

Wasan da za'ayi yau kuwa sune; Barcelona, zata Kara da Osasuna, sai Leganes zata karbi bakuncin Las Palmas,Valencia zata fafata da Real Sociedad, Deportivo kuwa zata kece raini da Real Madrid ne.

Za'a buga wasannin a lokuta daban daban agogon Najeriya da Nijar tun daga karfe shida da rabi na yamma har zuwa takwas da rabi na dare.

A kasar Ingila kuwa, jiya kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta lallasa Southampton da kwallaye 4-2, a ragowar wasannin Firimiya da ba ayiba saboda wasu dalilai.

A yau kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, zata kara da Leicester City, Middlesbrough's da Sunderland, sai Crystal palace zata karbi bakuncin Tottenham, da misalin karfe takwas saura kwata agogon Najeriya da Nijar.

A bangaren saye da sayarwa kuwa Barcelona tana zawarcin Dele Alli daga kungiyar Tottenham, Real Madrid ta shiga neman D Senchez, daga Ajax, PSG tana cikin sahun zawarcin dan wasan Sevilla, mai suna Vitolo.

Valencia na bukatar dauko aron dan wasan Real Madrid, mai suna Marcos Llorente, Bayern Munich, ta shiga sahun zawarcin Alex Sanchez daga Arsenal, PSG na shirin sayen Jorda Alba, daga kungiyar Barcelona.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG