Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Na Yunkurin Kirkiro Na'urar Da Za Ta Rika Daukar Bayanai Daga Kwakwalwar Mutum


Shafin sada zumunta na Facebook ya bayyana cewa wata tawagar Injiniyoyi 60 suna nan suna aikin kera wata na’urar kwamfuta da zata rika yin mu’amula da kwakwalwar mutum, ta yadda da zarar ya yi tunani zata rubuta abin da ke cikin zuciyarsa.

Tawagar Injiniyoyin dai na shirin yin amfani da wata fasaha da za ta rika daukar bayanai daga kwakwalwar mutum cikin dakika, ta kuma mayar da abin da mutum yake tunani cikin rubutu.

Shugabar wannan tawaga Regina Dugan, ta bayyana cewa abin da suke fatan yi shine su samar da hanyar da mutane za su rika rubuta kalmomi 100 cikin minti ‘daya kawai ta hanyar yin tunani, wato ninki biyar kenan wajen sauri idan aka kwatanta da yadda mutane suke rubuta kalmomi ta kan wayoyinsu.

Sannu a hankali dai wannan na’ura za ta baiwa mutane damar sarrafa na’urorinsu da zuciyarsu, maimakon su yi amfani da hannunsu wajen danne-danne kamar yadda aka saba.

Ga karin bayani a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG