Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atletico Madrid Zata Kara Da Villarreal A Laliga 2016/17 Mako Na 34


A jiya litinin 24/4/2017 an gwabza a wasa daya tilo da ya rage bangaren laliga mako na talatin da ukku, kungiyar kwallon kafa ta Eibar, ta sha kashi a hannun Athletic Bilbao, da ci 1-0.
Sai kuma yau a cigaba da wasa a matakin mako na talatin da hudu a bangaren laliga na shekara 2016/17, Sporting Gijon, zata karbi bakuncin Espanyol,
Granada, a gida zata gwabza da Malaga, sai Atletico Madrid, zasu kara da Villarreal, za'a buga wasanninne alokuta daban tun daga misalin karfe shida da rabi na yammaci har zuwa takwas da rabi na dare agogon Najeriya, Nijar kamaru da kasar Chadi.

A bangaren saye da sayarwa na dan wasan kwallon kafa ta duniya kuwa
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, tana zawarcin dan wasan Tottenham, dan kasar Ingila, mai suna Dele Alli.

Lyon, tana shirin sayen dan wasa daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, mai suna Antonio Martial, Sevilla ta kasar Spain, tana neman dan wasa mai tsaron baya na Roma Bruno Peres.

Ita kuwa kungiyar Manchester United, ta shiga sahun neman dan wasan tsakiya na Monaco Bernardo Silva, Real Madrid tana zawarcin Cencelo daga Valencia.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG