Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Muryar Amurka Ta Sami Bidiyon 'Yan Boko Haram? - Leo Keyen


Kamar yadda muka tattauna akan zaman tare da kyautatawa juna a shirinmu na yau da gobe shirin matasa, a wannan karon mun sami zantawa ne da shugaban sashen Hausa na muryar Amurka, akan hotunan bidiyo da muryar Amurka ta nuna kwanaki kadan da suka gabata inda ya amsa tambayar da yawancin masu sauraron mu suka tambaya, kamar haka, shin ya a akayi muryar Amurka ta sami wannan bidiyo? sai ya ce;

Da farko bari in fara da gaisuwa da jinjina ga masu saurare da kallon shirye shiryen VOA Hausa-Radio, da talabijin da kuma yanar gizo, Musamman ma yanar sada zumunta da suka kashe dumbin kudadensu suka sayi data domin su kalli bidiyon da VOA, albarkacin shashen hausa ya kwakwulo akan akidar ta’addancin Boko haram.

Ta’addancin da suka aiwatar ko kuma dai ince suke ci gaba da aiwatarwa a arewacin Nijeriya, da bangarorin, Nijer da kamaru da chadi, tsabar ta’addanci da ya kumshi kisa da hallaka al’umma, da kai hare hare a kan mazauna karkara da yaki da rundunonin sojojin hukuma.

Tada boma bomai a masallatai da coci-coci da tashoshin mota, sace-sacen mutane, musamman ma mata yara matasa, da matasa na karkara da ‘yan makaranta. Sace-sacen arziki da kaddarorin manoma da makiyaya.

Duk dai don su tilastawa mutane ko su tsoratar da al’umomin kasashen nan da na ambata su yarda da wata daula wadda ni har ga Allah ba addinin islama bane.

2. KO INA MURYAR AMURKA TA SAMO WANNAN BIDIYO DA ‘YAN BOKO HARAM SUKA DAUKA DA KANSU?

Masu saurare saboda dalilai da yawa da suka hada da kare sirri ko kuma mutunta hakki ko kuma martabar wadanda suke bamu, da kuma dalilin binciken dokar aikin jarida, ga wadanda suka karanta ko kuma suka kware a aikin jarida ya hana mu fallasa tushen labarin mu. Saboda haka a shugabance da wuya in fadi inda muka bankado wannan bidiyon.

Amma a matsayi na shugaban sashen Hausa, ina so in shaidawa malamin da yayi tambayar cewa makasudin aikin dan jarida shine bincike da watsa rahoto akan abinda ka iya hallaka dan’adam, ko kawo wa al’umma ko kasa matsala domin al’umma tayi hattara.

Shiyasa a nan Amurka, kafin ka fara aikin jarida musamman ma VOA sai ka/kin rantse zaka kare demokradiya kuma ba gudu ba ja da baya, zaka fadi gaskiya kuma zaka yi adalci ga duk bangagorin da binciken naka ko naki ya shafa.

Kenan banbancin dan jarida da dan ta’adda a rantsuwa yake, dan ta’adda shi rantsuwar halaka al’umma yake daukakawa shi kuma dan jarida rantsuwar habaka Al’umma yake.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG