Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salman Khan Ya Birge Masoya


Salman Khan
Salman Khan

Salman Khan, ya birge masoyan sa a kasar Australia da New Zealand, a ci gaba da rangadin Da –Bangg, da yake yi, inda ya chashe da rawa irin daban daban dama can an san Salma Khan, da irin yake taka rawa.

A lokacin da ya fito ya fito sanye da bakaken kaya su kuma sauran abokan rawarsa suna sanye da fararen kaya sa’ilin nan fitilar da aka haska mai kalar shudi ne abinda ra birge masu kallo, suka dinga Shewa

Zai kuma nufi birnin Sydney da na Melboutne, jama’a na son ganin sa a Brisbane amma kash sai dai birnin na Brisbane, bay a cikin biranan da aka tsara zai ziyarta.

Salman Khan ya birge masoyansa da irin takun rawarsa da suke son ganin kamar wanda yayi a tare da Mari Maria a shekarar 2007, wanda a duk lokaci yayi ta a faggen rawa tafkar sabuwace.

Masu kallo su cika da kuma Shewa ta kowane bangare na nuna jin dadi da annashuwa da yadda ya birge su abin sai wanda ya gani.

XS
SM
MD
LG