Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Fara Wasannin La Liga Na Kasar Spain Da Zafi-Zafi


Lionel Messi
Lionel Messi

A yau Jumma'a 17 ga watan Agustan shekarar 2018 za'a fara fafatawa a wasannin La Liga na kasar Spain, na shekarar 2018/19 mako na farko.

Wasan farko zai gudana ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Girona da takwararta kungiyar Real Valladolid, da misalin karfe bakwai da minti sha biyar na yammaci Agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.

Da misalin karfe tara na dare, Real Betis zata kece raini da Levante. A bangaren saye da sayarwar ‘yan wasan kwallon kafa kuwa, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, taki amincewa da ta sayar da dan wasan Faransa mai shekaru 25, da haihuwa Paul Pogba, wanda ke son canja sheka zuwa kungiyar Barcelona.

Ita ma Arsenal ta ce tana da tabbacin cewa zata iya rike dan wasan tsakiya na kasar Wales, Aaron Ramsey, mai shekaru 27, a duniya duk da sha'awar da kungiyoyi irin su Barcelona, Lazio da kuma wasu na Super League na kasar Sin, Suka nuna akan dan wasan.

Dan wasan Manchester United, Romelu Lukaku, mai shekaru 25, da haihuwa ya ce zai yi ritaya daga kwallon kafa ta kasa da kasa amman sai bayan da dawowa daga wasannin cin Kofin Nahiyar Turai 2020.

Real Madrid, ta bayyana bacin ranta kan kungiyar Inter Milan ta kasar Itali bisa yadda ta tuntubi dan wasanta Luka Modric, mai shekaru 32 a duniya ta bayan gida ba tare da ta same ta ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG