Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lionel Messi Ya Cika Kwallon Sa Ta 600


Dan wasan dankasar Agentina wanda ya ke fafata wasan sa a kungiyar kwallon Kafa ta Barcelona a kasar Spain, ya sami wannan nasaranne a ranar lahadi 4/3/2018 a wasan da suka yi da Atletic Madrid, bangaren Laliga mako na 27, inda suka doke Atletico Madrid da ci 1-0, Messi ya jefa kwallon cikin minti na 26 da fara wasan daga tazarar yadi 25 zuwa ragar.

A jimillar kwallaye Messi ya zurara kwallaye 539 a kungiyar Barcelona ya kuma jefa kwallaye 61 a kasar sa ta Argentina inda ya hada jimillan kwallaye 600 dai dai inda a bangaren Laliga na bana yake kan gaba da kwallaye 28.

A dukkan nin wasannin da Messi ya buga kuwa a wannan shekarar ya zurara kwallaye 100 a raga.

Kungiyar ta Barcelona dai ta na saman teburin Laliga da maki 69 ta haura kan mai beye mata Atletico Madrid da maki 8. A ranar Asabar zata kara da Malaga a wasan mako na 28 a Laliga kasar Spain.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG