Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Zawarcin Lionel Messi


Shugaban kungiyar kwallon kafar Argentina Claudio Tapia, ya bayyana cewar Lionel Messi, dole ya ci gaba da bugawa kungiyar kasarsa wasa, domin kuwa kungiyar na samun karin kudaden shiga a duk lokacin da ya buga wasan.

Ya zuwa yanzu dan wasan dai bai bayyana makomarsa ba akan kungiyar ba, tun bayan kashi da kungiyar ta sha a wasan cin kofin duniya zagaye na 16, wanda kasar Faransa ta fitar da kungiyar.

Amma ya bayyana cewar kafin kakar wasannin ta zagayo, za su yi haka don su sami nasara a wasa. Kodai suci wasa a wannan karon ko kuma su zama ‘yan kallo. Ya samu kan shi cikin wani yanayi na rashin jin dadin yadda basu yi nasaraba a gasar cikin kofin duniya.

Amma kungiyar ta bayyana muhimacin dan wasan a garteta, musamman idan aka yi la’akari da irin kudaden shiga da kungiyar ke samu.

Shugaban kungiyar Tapai, ya samu haduwa da dan wasan a makon da ya gabata.

Haka Kuma ya bayyana cewar dan wasan yana bukatar lokaci, don ya yi nazari ko zai dawo kungiyar. Ya kara da cewar muna da kyakyawar danganta da dan wasan, yanzu haka dai yana hutu inda yake jin dadinsa tare da iyalan sa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG