Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawaitar Amfani da Robot Nada Ban Tsoro Ga Rayuwar Dan-Adam


Ana cigaba da samun karuwa da inganta mutun mutumi a duk fadin duniya, wadanda ake kirkiror su da zummar yin aiki kafada da kafada da mutane a ma’aikatu. Hakan na nuni da cewar sai an inganta robot din don yin aiki kamar mutun,da yini tafiya kamar mutun, da kuma maida komi nashi kamar na mutun.

Yadda ake kera mutun mutumin da suke matukar kama da mutun, abun nada ban tsoro matuka. Wasu mutane na ganin hakan barazana ce ga lafiyar su harma da aikinsu, domin kuwa baza iya jurema zama cikin daki tare da mutun mutumi yana kallon su ba.

Hatta masu bincike da bibiyar hanyoyin da za’a bi don inganta shi basu samun natsuwa wajen gudanar da mu’amala da robot din..

Farfesa Jonathan Gratch, darakta a tsangayar kirkirara na’urorin zamani na jami’ar kudancin California, daya daga cikin masu gudanar da bincike yadda za’a inganta mutun mutumi, yace Na san yadda suke aiki da kuma irin yadda aka tsara tunaninsu, na san da cewar mutane suke basu umurni irin aikin da zasu gabatar, amma duk da haka bana samun natsuwar zama da su a cikin daki, na’urorin zamani na jami’ar kudancin California.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG