Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a Sun Fara Korafi A Kan Sabuwar Wayar Samsun Galaxy Note 9


Masu amfani da sabuwar wayar hannu da kamfanin Samsung ya kaddamar makwanni kadan da suka gabata da ake kira Samsun Galaxy Note 9, sun fara korafi akan yadda manhajar daukar hoton wayar ke da matsala, kammar yadda da dama suka bayyana cewa sun fuskanci irin wannan matasala.

Wani daga cikin kwastomomin wannan kamfani ya bayyana a shafin mujallar Forbes, cewar a ganin shi wannan matsala ce da kanfanin zai iyan magancewa ta yanar gizo ba lallai sai an kwance ko bude wayar ba.

Matasalar wannan waya dai kamar yadda mutanen da suka fara amfani da ita suka bayyana shine, mahajar daukar hoton ke makalewa da zarar an dauki hoto da ita, wasu sun bayyana cewa basa iya daukar hotuna da dama a lokaci guda sai manhajar ta makale da kanta.

Ana sa ran kamfanin zai dauki mataki cikin gaggawa domin magance wannan matsala da ta bayyana cikin dan kankanen lokaci wadda ka iya kawo cikas musamman ga masoya kanfanin da kuma wadanda kanfanin ya ja hankalin su musamman wadanda suka fara amfani da sabuwar wayar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG