Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Na Neman Wasu Matasa Ruwa A Jallo


Rundunar ‘yan Sandan jihar Enugu ta baza komarta tana neman wasu matasa da ake kira “Malaysian Boys” ruwa a jallo.

Kakakin rundunar SP Ebere Amaraizu, ne ya bayana haka a wata sanarwa ta rundunar ta fitar, ya kuma bukaci jama’a dasu gaggauta sanarda hukumar duk wani labara da ka iya taimakawa wajen damke wadannan matasa.

Sanarwar ta kara da cewa matasan na iya kai kansu ga ‘yan Sandan farin kaya wayau CIID, na rundunar ta jihar Enugu.

Su dai wadannan matasa sune Ikechukwu wanda ake kira Master, Okoro Ifeanyi wanda ake kira Bukar da Mathew Marcel Ojilke, Ogbode Ajulu, Odumodu wanda ake kira Asogwa, Mike da shima ake kira Anyi Anyi da Hyacinth Ugwu Julius.

Sauran sun hada John Okwelli, Anselem da aka fi sani da Photo, Ikechukwu Aaron, Nnamdi Michael, Gabriel da ake kira Gabos da kuma Fela, Zero, Akwasa, Mmiri da Ratty.

Rundunar tace wadannan matasa sun addabi jama’ar yankin inda suke tafka masu ta’asa iri iri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG