Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Fado Ya Mutu Daga Kan Dutse Garin Kallon Wayar Hannunsa


Wani mutumi ya fado daga kan wani dutse har na tsawon kafa 40 ya mutu a birnin San Diego dake Jihar California a Amurka, a saboda hankalinsa ya tafi wajen kallon wata na'urar da yake rike da ita a hannunsa.

Masu aikin ceto mutane daga cikin ruwa a San Diego, sun ce mutumin mai shekaru 33 da haihuwa, yaje shi bakin wannan Dutse na bakin teku da ake kira Sunset Cliffs tare da wani fasinja a cikin mota, domin kallon yadda rana ke faduwa a bisa teku. Da ya rasa inda zai ajiye motarsa ne sai ya fita da kafa yana zagayawa domin ya ga ko zai samu wurin saka motar, ya bar abokin tafiyarsa cikin mota.

Shaidu suka ce sun ga mutumin yana duba wani abu a hannunsa, watakila wayar hannu ce ko kyamara, babu wanda ya tabbatar, kuma hankalinsa na jikin wannan na'urar ne har ya kai ga gefen wannan dutse bai sani ba, ya fada kasa.

Mutane uku sun sauka kasa ta kan wannan dutse inda suka yi kokarin farfado da mutumin, amma suka kasa.

Likitocin gaggawa sun same shi a mace a wurin.

Jami'in masu aikin ceto mutane daga ruwa a San Diego, Saje Bill bender, yace mutumin ya mutu a sanadin wani kuskuren da mutane da yawa suke aikatawa. Yace, "kamar yadda ba a son mutum yana tuka mota yana amfani da wayarsa, haka ma ba a son mutum ya maida hankalinsa kacokam kan wayarsa a lokacin da yake tafiya da kafa.

Ya kara da cewa, "bai kamata idan mutum yana wurin da zai iya fuskantar hatsari, ya maida hankalinsa a kan wani abu dabam ba."

XS
SM
MD
LG