Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Masu Fashi Da Makami 375 An Kuma Kwato Motoci 233


Rundunar ‘yan Sandan,jihar Lagos, ta dakile afkuwar fashi da makami har 125, ta kuma kwato motoci 233, da kama masu satar mutane 25, da kuma ‘yan fashi da makami 375, an kuma kashe ‘yan fashi 40, a musayan wuta da ‘yan Sanda, inda aka ceto mutane 24, da aka sace.

Rundunar ta kuma cafke ‘yan kungiyar asiri 113, Sojan gona 7, masu satar albarkatun Mai 10, an kuma kwato bindigogi iri daban daban guda 216 da jiragen ruwa masu dauke da bindiga guda 2, da kwale kwale 2, da kuma albarusai da dama da kuma kayayyaki iri daban daban na fiye da Naira biliyan 1 da miliyan 300.

Kwamishnan 'yan Sandan jihar Lagos Fatai Owoseni, ya ce tuni da dama a cikin wadanda suke hannu suka gurfana a kotuna daban daban.

A wani labarin kuma an samu fiye da kararraki 200, na kisa daga watan Janairu zuwa watan Nuwamba na wannan shekarar da muke ciki a jihar Lagos.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar, Lagos, Fatai Owoseni, wanda ya bayana haka a wajen wani taro akan tsaro ya ce akasarin kashe kashen sun faru ne a tsakanin ‘yan kungiyar asiri da kuma fada a unguwani.

XS
SM
MD
LG