Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarauniyar Kyau Ta Duniya A Cikin Minttoci 3 Kuskure Ne!


A duk shekara akanyi bukin fitar da macce da tafi kyau a duniya, wanda ‘yan mata masu kyau a duk fadin duniya sukan halarta, wannan shekarar an gudanar da shi a kasar Amurka ne. A lokacin wannan bukin akanyi amfani da abubuwa da dama wajen zabar wadda ta zama gwarzuwar shekara. A lokacin akan tambayi kowace ‘yar takara abubuwa da zatayi idan tazama gwarzuwa, wanda suka hada da ayyukan taimakon marasa karfi a duniya da dai duk abubuwa da suka kamata ace mutun yayi wajen bada taimako ga al’uma.

Duk wadda tasamu nasarar lashe wannan gasar za’a bata kambun macce da tafi kyau a duniya har na tsawon shekara daya. Amma a karon farko anyi sarauniyar kyau ta mintoci 3. Hakan ya faru ne a dai-dai lokacin da mai gabatarwa na shirin yayi kuskure wajen faden suna, bayan an tantance cikin ‘yan-mata fiye da 50 daga kasashe fiye da 100 a duniya, zuwa ‘yan-mata 2 da suka rage da ‘yar kasar Colombia da ‘yar kasar Philipian.

Dai-dai lokacin da mai gabatarwa ya fadi cewar ‘yar-kasar Colombia ita, ta lashe kambun na wannan shekarar kuma har ansaka mata kambun macen da tafi kowacce kyau a duniya, bayana mintoci 3 sai aka jawo hankalin mai gabatarwan da cewar ba itace ta lashe gasarba, hakan yasa mai gabatarwan ya dauki alhakin kuskuren. Daga nan sai aka cire kambun daga kan ‘yar kasar Colombiar da tazo ta biyu aka maida ma ‘yar kasar Philipian.

Hakan dai ya kawo rudani kwarai da gaske, wasu na gani haka bai dace ba, kamatayayi ace ya tsaya ya lura da kyau kamin yayi wannan sanarwar. Amma hakan da yayi ya kawo matsaloli da dama, don kuwa wasu da dama na ganin cewar kamata yayi ‘yar kasar Colombia ta garzaya zuwa kotu, don kwato hakinta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG