Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

West Ham Ta Yi Watsi Da Bukatar Swansea


West Ham ta yi watsi da bukatar kungiyar Swansea ta dawo da tsohon dan wasan gabanta dan kasar Gana Andre Ayew 28, wanda ya bar kungiya a shekara 2016 bayan ya ci musu kwallaye 15 a kungiyar.

Stoke city ta sa fam miliyan £3.25 wajan sayen dan wasan gefe na Kungiyar New York city mai suna Jack Harrison, 21 wanda ya buga wasa a tawagar matasa ta liverpool da Manchester united.

Alamun na nuwa kungiyar Manchester united zata shiga damuwa ganin cewar yanzu Real Madrid, zata karkato alkalan ta kan mai tsaron ragar kungiyar David de Gea, ganin cewar Real ta Gaza sayen Golan Athletic Bilbao Kepa arrizabalaga.

David de Gea dai har yanzu bai sabunta kwantirakinsa a kungiyar ta Manchester ba inda zai karkare a karshen kakar wasannin badi.

Kocin Newcastle United, Rafael Benítez ya ce yana da bukatar sayen ‘yan wasa har guda uku ko hudu nan da kwanaki goma kafin a rufe cinikayyar ‘yan wasan kwallon Kafa na watan janairun wanna shekara, Crystal palace ta ce tana bukatar Karin akalla dan wasan gaba guda daya a watan janairu nan inda ta nuna sha'awarta kan dan wasan gaba na Inter Milan mai suna Eder 31.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG