Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Kano Pillars Steven Eze Ya Samu Hayewa Gaba


Sabon dan wasan baya na kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars dake tarayyar Najeriya, Steven Eze, ya sanya hannu kan wata kwangila bisa yarjejeniyar da kungiyar kwallon Kafa ta Lokomotiv Plovdiv, dake kasar Bulgaria.

Dan wasan ya sanya hannu a wannan satin kan yarjejeniyar da aka yi tsakanin wakilin sa Dr Ojore Oka, da Lokomotiv Plovdiv.

Dan wasan Steven Eze, wanda yanzu haka yake cikin tawagar ‘yan wasan Najeriya, da suke fafatawa a gasar wasan (CHAN) a kasar Morocco ya zo kungiyar Kano Pillars, ne a matsayin rance bayan ya kammala kwantiraginsa da kungiyar kwallon Kafa ta Ifeanyi Ubah, tare da yarjejeniyar cewa lokacin da ya samu wani abu za a sake shi ya tafi.

A ta bakin jami'in yada labarai na Kano Pillars Rilwanu Idris Malikawa, ya tabbatar da wannan labari inda ya ce tuni dai hukumar kula da kwallon kafa ta Kano Pillars (Sai masu gida) ta yi masa fatan alheri.

Steven Eze, zai shiga sabon kulob din a kasar Bulgaria da zarar an kammala gasar CHAN ta nahiyar Afirka da akeyi a kasar Morocco.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:18 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG