Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mutum Ya Tsinci Bahun Kudi Kuma Ya Dawowa Da Mai Kudin


 hryvnias-dollars
hryvnias-dollars

Wani mutum mai suna Kennedy dake jihar Utah a Amurka, yayi mamaki alokacin da ya tsaya a wata babbar hanya domin ya ture wani bahu daga kan hanya don kare sauran motoci masu tafiya daga hatsari.

Mutumin yace, “na ‘dauka bahun bashi da nauyi, na mika hannuna domin na ‘daga bahun amma na kasa.”

Bahun dai yana da tsayin ‘kafa hudu da fadin kafa biyu, kuma yana cike kudi dalolin Amurka, cikin wasu kananan ledoji wanda suke ‘dauke da takardun daloli hamsin, dari. Kiyashin kudin dake cikin duk leda daya ya kai dalar Amurka dubu ashirin da biyu, har yanzu dai ba’a san ko nawa ne kudin dake cikin buhun ba.

Kennedy yayi kokarin neman motar da kudin ya fado daga cikin ta amma bai samu sa’a ba. Ya kuma dauko kudin zuwa gurin aikin sa, ya kira ‘yan sanda.

‘yan sanda uku ne suka zo gurin Kennedy bayan da ya kira su, sunyi mamakin ganin kudi dayawa a cikin bahu, ‘daya daga cikin ‘yan sandan mai suna Brady Zaugg yace, “tunda nake ban taba jin ance bahun kudi ya fado daga bayan wata mota kamar haka ba, wannan wani abune dake faruwa a wasan kwaikwayo.”

Kudin dai ya fado ne daga motar wani kamfani mai dakon kudi da ake kira Brink’s, ma’aikatan dake tukin motar alokacin da kudin ya fado sun gayawa ‘yan sanda cewar sun bi kan wata gargada ne akan hanya, amma basu lura da cewa ba kofar baya ta bude kuma kudin sun fadi.

Kennedy yace har yanzu bai ji maganar wani tukuicin tsuntuwar kudin ba daga kamfanin na Brink’s.

Amma shi bai damu da komai za’a bashi ba, shi dai yayi abinda ya kamata.

XS
SM
MD
LG