Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sana'o'i ta Shafin Yanar Gizo Tafi kawo Riba


Whatsapp
Whatsapp

Hanyoyin sadarwa na zamani na taima kawa matuka wajen sada zumunci dama tallafawa rayuwar dan’adam. Ta bakin Rahama Usman, wata yarinya ‘yar makaranta, wadda take amfani da shafufukan ta na facebook da wazob don tallata hajojinta ga abokai da mabukata, ita dai tafara wannan sana’ar tatace shekaru biyu da suka wuce.

Kuma takan sayo kaya daga mutane da kanje kasashen waje su siyo kaya ita kuma sai ta sa a shafinta na yanar gizo wanda daga nan sai mutane su gani idan suna da sha’awa sai su siya. Kuma ta hakan tasamu alkhairi matuka, don ta wannan hanyar takan samu kudin kashewa da nayi lalurorinta a makaranta da ma rayuwa batare da ta nema daga wajen iyayenta ba.

Akan siya kayanta a samata kudi a asusun ajiyarta na Banki, wasu kuma sukanzo gida su gani su biya kana ta basu. Ta kara da cewar bata wani wahala wajen tallata hajarta ko kuma ta biya wasu kudade don talla. Don haka tana kira ga mata ‘yan’uwan ta da su dage sunemi sana’a kada subari a barsu a baya wajen kasuwanci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG