Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ina Koyo Ne Daga Gurin Enyeama – Inji Akpeyi


Nigeria's goalkeeper Vincent Enyeama seems to defy gravity in the net for Nigeria at the Brasilia national stadium in Brasilia, June 30, 2014.
Nigeria's goalkeeper Vincent Enyeama seems to defy gravity in the net for Nigeria at the Brasilia national stadium in Brasilia, June 30, 2014.

Daniel Akpeyi ya amince cewa akwai sauransa kafin ya zama mai tsaron gida na Super Eagles Vincent Enyeama.

An dai kira Akpeyi daga kungiyar Warri Wolves, satin daya wuce bayan da mai tsaron gida Vincent Enyeama ya sami matsalar ciwon baya, kafin wasan ‘kawancen da zasuyi da kasar Afirka ta Kudu.

Akpeyi yayi kokari sosai inda ya kare kwallaye dayawa daga shiga raga, ya kuma tabbatar da Eagles ta kasance a wasan.

Tun daga nan ake ganin shine zai maye gurbin Enyeama, amma yace yana koyo ne daga gurin manya wato Enyeama.

Akpeyi yace, “ina matukar farin ciki da wasan da nayi, amma har yanzu ina koyo ne daga gurin masu tsaron gida, daga cikin su kuwa harda Vincent Enyeama kuma bana ‘daukar kaina a matsayin kwararren ‘dan wasa tukunna. Har yanzu ina da sauran tafiya, kuma bazan bar wasa ‘daya ba ya hura min kai ba.”

Ya kuma yi amfani da damar sa wajen godewa duk ‘yan wasan Super Eagles, domin damar da suka bashi nayin wasan daya nuna kwazonsa.

Inda yace, “ina godiya ga Koch Dan Amokachi da sauran Koch din Eagles, domin bani dama da sukayi, kuma koda yaushe a shirye nake na wakilci Najeriya a ko’ina duk lokacin da aka kira ni.”

XS
SM
MD
LG