Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Waka Ta Wa'azi Ce Ga Matasa -Inji Abdul Actor


Abdul Actor
Abdul Actor

Abdullahi Abdulhamid wanda aka fi sani da Abdul Actor, ya ce yana wakokin da suke wa’azantarwa ga matasa kan muhimmanci yin sana’a domin zama masu dogaro da kai, ya ce inda ya bada misali da wakarsa da yayi mai suna Sana’a sa’a.

Matashin ya kara da cewa ya tsinci kansa a harkar ta waka sakamakon bin wasu mawaka da yake yi a wancan lokaci sannan sai ya lura yana waka ba tare da ya rubuta ta ba wanda ya gane cewa wannan da Allah ya bashi kuma za a dama da shi a masana’antar ta mawaka

Ya ce baya ga wakokin sa sun karkata kan fadakarwa ta sana’a ko rayuwar matasa, ya bayyana cewa babban kalubalen da yake fuskanta shine matsala ta studio da yake recording wakarsa kasancewar bashi da studio nasa na kansa yana fuskanta tsaiko

Daga karshe ya kara da cewa rashin studio na daya daga cikin abubuwan da ke kawo wa harkar barazana a mafi yawan lokuta sai an bi layi ga.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG