Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jabir S TOFA: Na Kan Wa'azantar Da Matasa Muhimmancin Rike Alkawari A Wakoki Na


Jabir S Tofa wanda aka fi sani da Top Son ya ce yana wakokin nanaye inda yake wa’azantar da matasa muhimmancin rike alkawari da kauracewa yaudara domin samun soyayya mai dorewa.

Matashin ya bayyana haka ne a yayin da ya ke zantawa da wakiliyar DandalinVOA a garin Tofa, inda ya bayyana cewa a waka, ya zabi wakokin nanaye domin a cewarsa ta nan ne zai fadakar da ‘yan uwansa muhimmancin zumunci da rike amana, ya ce ya lura da cewar akwai gyara a yadda matasa ke mu’amalarsu a yanzu.

Jabir ya ce, akwai muhimmanci matasa su daina kulla alakar da ba ta da amfani kuma ba zata haifar da wata riba ba tare da jan hankalinsu wajen tabbatar da duk budurwar da zasu kulla alaka da ita su tabbata zata kai su ga aure.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:49 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG