Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Kan Fuskanci Kalubale Da Dama A Wuraren Aiki- Inji Barista A'isha Tijjani


Barista A'isha Tijjani
Barista A'isha Tijjani

Babban kalubalen mace ma’aikaciya shine yadda abokan aiki maza ke yiwa mata kallon basu cancanta ba, a mukaman da suke rike dasu a wuraren ayyukansu inda suke neman tunkude mata gefe domin wani kudiri nasu a ko da yaushe inji barista Aisha Alh Tijjani.

A mafi yawan lokuta mata a irin wadandan lokuta kan karaya da zarar sun fara fuskantar takura daga abokan aikin su maza har ta kai su ga sun janye ko sun hakura da aiki ma gabaki daya.

Ta kara da cewa saboda dabi’ar nan ta malam Bahaushe na cewa a koda yaushe namiji shi ke gaba da mace , don haka dole ta janye ta barwa maza dama a wuraren ayyuka.

Barista ta ce, tana samun kalubale daga fannin dalibai, ganin cewar daliban sun yi yawa a wasu loktuan akan fuskancin 'yar gwagwarmaya kafin a shawo kan su mussaman ma a wannan lokaci da wayoyin salula da makamantansu

Ta ja hankalin mata da su jajirce wajen neman ilimi, zancen mace ta jira jin dadin rayuwa daga miji ko samun jin dadi abu ne mai kama da tatsuniya amma da zarar ta nemi ilimi mace zata yi yadda ta ke so da ilimin nan nata.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG