Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Waka Ce Hanya Mafi Sauki Wajan Fadakarwa Da Ilimantarwa - Hassan K-Boys


Hassan K-Boys
Hassan K-Boys

Na fara waka saboda sha’awa ba don tara abin duniya ba kuma na baiwa kaina lokacin da zan daina, kuma abinda ya faru Kenan a cewar mawaki Hassan Muhammad Auwal, daya daga cikin mawakan K-boys a Da.

Hassan ya bayyana cewa a wancan lokacin da yake waka tare da kungiyar K-boys, sunyi fice kuma wakokinsu sun raja’a ne a kan abubuwan da ke faruwa ga al’umma mussamam ma matasa.

Matashin ya kara da cewa tunda farko dama bai sanya a ransa zai dauki waka a matsayin sana’a ta dindindin ba, kuma lokacin da ya debawa kansa na cika ya fito gidan rediyo ya bayyanawa duniya cewa ya daina waka.

A cewarsa bai dauki waka tamkar kasuwanci ba, kuma ya ce waka na daya daga cikin abubuwan da ke kawo sauyi ga rayuwa a cewarsa ita ce hanya mafi sauki ta fadakarwa da kuma ilmantarwa

Hassan ya ce wakokin raps na nusar da gwamnati da ma al’umma dangane da wasu dabi’u marasa kyau ko da yake bukatar a waiwaya da gaggawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:54 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG