Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sun Ci Zarafin Wata Matashiya


Wasu matasa biyu sun gurfana a gaban kotun bisa zargin yiwa wata matashiya mai shekaru goma sha hudu fyade a jihar Ekiti.

Matasan Olajire Ayoade, mai shekaru goma sha takwas da Tope Owoeye mai shekaru goma sha tara sun yiwa yarinyar fyade ne bayan da ta ki amincewa da bukatarsu.

Mai gabatar da karar Johnson Okuade, ya shedawa kotu cewa matasa sun aikata laifin ne a ranar 8, ga watan Fabarerun wannan shekara a layin Afao dake Ikere-Ekiti, abinda ya kai ga har sai da aka kwantar da ita a asibiti.

Ya kara da cewa laifin ya sabawa sashe na 516(31) mai nasaba da hakkin yara na jihar Ekiti, na shekarar 2012.

An mika takardun shara’ar ga ofishin daraktan mai kula da manyan laifuffuka domin bada shawara akan mataki nag aba.

Alkalin kotun Aderopo Adegboye, ya dage sauraren karar zuwa ranar juma’a mai zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG