Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Maciji Ya Hadiye Naira Miliyan 36


Hukumar jarabawa ta JAMB, ta dakatar da wata ma’aikaciyar hukumar mai suna Philomina Chieshe, a bisa wasu makudan kudade Naira miliyan talatin da shida (N36), wadanda aka ce wai maciji ya hadiye a offishin hukumar dake jihar Benue.

Jami’in yada labarai na hukumar ta JAMB Fabian Benjamin, ya shedawa jaridar Punch, cewa baya ga dakatar da ita hukumar na daukar wasu matakan ladaftarwa, baya ga binciken da jami’an tsaron ke cigaba da yi akan abinda ta ce wai maciji ne ya hadiye Naira miliyan talatin da shida a ofishin JAMB, dake jihar Benue.

Daga bisani kuma sai ta ce mai aikin ta ne da hadin bakin wata mata Joan Asen, suka sace kudin da asiri daga ma’ajin kudi na ofishin .

Koda yake hukumar EFCC, ta fara binciken lamarin, bayan da majalisar zartarwar Najeriya a bara ta ce yakamata a binciki JAMB.

Ministar kudi ta Najeriya Kemi Adeosun, a lokacin da take jawabi ga majalisar zartarwa a bara ta ce hukumar JAMB, ta baiwa gwamnatin Naira biliyan biyar da alkawarin cika sauran Naira biliyan uku, inda a baya hukumar ke baiwa gwamnati Naira miliyan uku a kowace shekarahar na tsawon shekaru arba’in, trace wannan wagegen gibin da aka samu ya sa tilas a binciki shuwagabanin baya na hukumomin biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG