Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Ruwa Mai Amfani Da Hasken Rana Ya Fara Zagayen Duniya


Jirgin ruwa na farko mai amfani da hasken rana, a fadin duniya zai tafi shawagi na tsawon shekaru shida. A zagayen da jirgin zai yi zai zagaye duniya, daga farkon wannan shekarar. Asalin jirgin na tsere ne, wanda aka canza shi zuwa jirgi mai amfani da hasken rana.

Jirgin yana dogara ne da wutar da zai samar ma kanshi, daga hasken rana da kuma karfin farfelan dake samar masa da wadatacciyar iska, da zai iya yunkura shi. An kiyasta kudin jirgin da cewa ya kai kimanin dallar Amurka $5.25M wanda ya yi dai-dai da Naira billiyan biyu da milliyan dari biyar da saba’in.

Jirgin yana bakin gabar teku a yankin Saint-Malo, na kasar Birtaniya daga inda jirgin zai fara tafiya, zai yi kuma yi tsaye-tsaye a kimanin tashoshi dari da daya, wanda suka hada da kasashe hamsin a fadin duniya, zai fara yada zango a kasar Paris.

A cewar Mr. Nicolas Hulot, kwararre a harkar muhalli, yace wannan wani yunkuri ne da yake nuna alamu, akwai nasara wajen kauracema amfani da mai a na’u’rorin tafiye-tafiyen zamani. Ya kara da cewar, duk wata matsala da ta shafi yanayi, duk hanyoyin shawo kan matsalolin suna nan kusa damu, haka dai na nuni da cewar, akwai bukatar zurfafa bincike.

Asalin jirgin an kera shi ne a shekarar 1983, karkashin shugabancin Mr. Mike Birch, jirgin dai ya samu lashe babbar kyautar Jules Verne a shekarar 1994.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG