Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararriyar Jaruma Ba'Amurka Debbie Reynolds Ta Rasu


Shahararriyar yar wasan fina finai Ba'amurka Debbie Reynolds ta rasu a jiya Laraba sakamakon matsalar bugun zuciya, kwana daya bayan rasuwar 'yarta ita ma tauraruwar fina finai Carrie Fisher.

Jarumar 'yar shekaru 84 Reynolds ta fadi da rana a gidan danta a yammacin Berverly Hills, dake California. Ankai Shahararriyar Jarumar Asibiti lokacin kadan bayan an kira motar Asibiti zuwa gidan dan nata.

Todd Fisher, Da ga Reynolds ya tabbatar da mutuwar Mahaifiyarsa ga kafafen yada labarai masu yawa inda yake cewa “Tana son ta kasance tare da Carrie”.

Ya kara da cewa “ Yanzu tana tare da Carrie kuma hakika zuciyoyin mu sunyi rauni” yake fada daga Asibitin Cedars- Sinai Medical Center, da ke birnin Los Angeles, inda aka dauki mahaifiyarsa a motar Ambulance, yace zafin mutuwar 'yar uwarsa yayiwa Renolds yawa.

Reynolds da Fisher, sun fito a cikin wani shiri na musamman da aka nuna a taron bikin fina finai na Cannes, a Faransa a farkon wannan shekarar mai taken “Bright Lights” an shirya fara nuna shi a tashar Home Box Office, a farkon shekarar 2017.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG