Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Auri Mahaifiyar Matarsa


Wani matashi mai shekaru ashirin da biyu mai suna Mahto Suraj, ya gujewa matasa mai suna Latila, a kuma auri mahaifiyar matar mai suna Asha Devi, mai shekaru araba’in da biyu.

Wani abin al’ajabi ya faru ne a lokacin da mahaifiyar matar ta kai masu ziyara, kamar yadda jaridar India Times, ta ruwaito Asha ta bar mijinta mai aiki a wata masana’anta a Delhi, ta auri mijin ‘yarta inda suka yi aure irin na gargajiya, da kuma na kotu.

Amma a yanzu Suraj, na neman a raba auransa da mahaifiyar matan saboda ya koma da tsohonwar matarsa Latila.

Ya kara da cewa yanzu ya gane kuskurensa da alkawarin cewa irin haka ba zai sake faruwa ba, yana mai cewa daga yanzu zai dauki Asha, a matsayin suruka.

XS
SM
MD
LG