Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauya Akalar Fina Finai A Kannywood


Balarabe Murtala Baharu kannywood
Balarabe Murtala Baharu kannywood

A yanzu masana'antar Kannywood ta canja salon fitar da fina-finan ta tsabanin yadda ake fitar da fim a da na kagaggun labarin mafi akasari da suka shafi soyayyar ko akasin haka, inji mai hulda da jama’a na kungiyar masu shirya fina finai Najeriya reshen jihar Kano, Murtala Balarabe Baharu.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA a Kano, inda yake cewa tuni masana'antar ta fara bin sahun cigaba na duniya ta hanyar fitar da fina-finansu a gidajen kallo na sinima da makamantasu

Baharu ya ce a da fina-finan da suke fiddawa sun fi raja'a ne kan soyayya da makamantansu, wanda a yanzu sukan dubi matsalolin da ke adabar al'ummar kamar matsalolin barace-barace ko shan kwayoyi tsakanin matasa, kabilanci da ban banci addini.

Ya kara da cewa fara hakan ke da wuya sai suka lura da sauyin tunanin alumma da irin sauyin kasuwannin fina-finai da hakan ya jawo masu, tare da ta'alaka hakan ga tasirin tauraron dan Adam, waztau Satelite da ake kalon fina-finai a kansu a yanzu.

Sannan hakan na baiwa masu shirya fina finai damar fasalta labarinsu ta adda mai kalo zai fahimta da kuma son binsa daki daki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:02 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG