Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rubuce Rubuce Babbar Hanyar Isar Da Sako Ga Al’uma


Bashir Yusuf Abubakar
Bashir Yusuf Abubakar

Wani marubucin littatafai wanda ya rikide mai rubuta fina finai, a Kannywood, Bashir Yusuf Abubakar, yace rubuce rubuce na bada damar isar da sako ga al’uma cikin tsanaki.

Yace babban matsalar da ya fara fuskanta a matsayinsa na marubucin fina-finan a baya a Kannywood, shine rashin biyansa hakkinsa bayan ya kammala rubutun fim,

Bashir Yusuf Abubakar wanda aka fi sani da Bashir Dan Rimi,ya kara da cewa da dama bayan ya rubuta fim sai kawai ya ga an fitar da fim din sannan a ki biyansa hakkinsa a kuma wajen rubuta sunan wanda ya rubuta fim sai kwatsam ya ga an rubuta sunan waninsa.

Dan Rimi ya kara da cewa a mafi yawan lokuta ya fi rubuta fina-finan barkwanci amma ya kan kuma duba wasu sassan rayuwa domin rubuta fina finai akai.

Ya ce a fim din sa da yake yi a yanzu ya waiwaiye matsalolin matasa, da zarar fun sami dama suka fara tara dukiya a wasu sassan duniya basau waiwaiyar gida balle ma suyi tunanin tallafawa tushensu kasancewar sun san cewar ana da karanci ilimin boko a sassan nasu.

Bashir dai marubucin littafai na Hausa, yace sha’awa ce ta kai ga rubuta fina finai don shima ya bada tashi gudumuwar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:53 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG