Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Satar Fasaha Na Mayar Da Kamfanonin Fina Finai Baya


Bashir Manda A Gurin Hada Wasan Fim
Bashir Manda A Gurin Hada Wasan Fim

Duniyar Kannywood dai ta alakanta satar fasaha da wasu mutane ke aikatawa a matsayin hanyar da take mayar da kamfanonin fina finai baya.

Hukumomin dake da alhakin kame wadanda ke satar fasaha sun gaza, inji Abdullahi Sani Abdullahi wanda akafi sani da Baba Karami alokacin da yake hira da wakiliyar Dandali Baraka Bashir, wanda ya bayyana mata cewar mutane na a duk lokacin da sa fitar da fim kasuwa mutanen na zuwa su sayi guda ‘daya tal, amma zasu je suyi ta kwafar sa har sai sun mai da shi sama da duba dari.

Har ila yau masu satar fasahar na amfani da wata hanya inda zasu je kasuwa suga fina finai nawa aka fitar a wannan satin to zasu sayo su ko guda nawa ne, sai kuma su mai da su cikin fefen dvd ‘daya tal Sukuma sayar da duk kwalliya daya cikin sauki.

Kasancewar babu wata hikima a yanzu haka da zasuyi domin dakile wannan satar fasaha wadda ta wuce addu’a, sabila da bangaren da gwamnati ta kafa domin yakar ire-iren wannan ayyuka bata iya tabuka komai.

XS
SM
MD
LG