Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jarumin Bayan Fage Na Duniyar Kannywood


A cikin shirin duniyar Kannywood Dandalin VOA ya sami zantawa da wani jazumin bayan fage, mutumin da ke fito da jarumai su fito cikin siffar da ya kamata.

Wakilyar Dandali Baraka Bashir ta zanta da Bashir Manda Brigade, wanda ya bayyana mata yadda ya tsinci kasansa cikin wannan sana’a ta harkar fina finai, inda yace sune ke yiwa jarumai kwalliya wadda ta hada da saka ciwo a jikin mutum lokacin da ake bukata da gemu da dai sauransu.

Sha’awa ce ta kai shi ga wannan sana’a inda ya kwashe shekaru biyar yana yi, duk da cewar bai je makaranta ba kan wannan harkar amma ya koyeta ne daga gurin maigidan sa Isa Alolo, ya kuma halarci wani taron karawa juna sani kan kwalliya wanda wasu turawa suka shirya a baya.

Fatan Mallam Bashir dai shine nan gaba ya zama mai bayar da umarni a harkar fina finai, a cikin kwalliya da yayi da tafi ‘daukar hankalin sa kuwa it ace ta wani sabon fim da aka hada amma haryanzu bai fito kasuwa ba sunan fim din “Ranar Juma’a” sai neme shi don ganin yadda wannan bawan Allah ya kware wajen yiwa jarumai kwalliya.

XS
SM
MD
LG