Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makaranta A Utah Ta Ware Hanya Domin MasuTafiya Su Na Amfani Da Waya


Texting While Walking
Texting While Walking

Wata jami'a a Jihar Utah a nan Amurka, ta kebe wa daliban da ba su iya rabuwa da wayoyinsu na hannu hanyarsu dabam, ta yadda zasu iya tafiya su na duba wayoyinsu ko amfani da su ba tare da sun ci karo da wani ba.

Amma kakakin Jami'ar Utah Valley, Melinda Colton, ta ce wadannan layuka da aka shata da launin kore mai haske a kan matakalar da ta shiga zuwa dakin motsa jiki, an yi su ne da nufin haskaka wurin da kuma janyo hankalin dalibai.

Da alamar wannan dabara ta su ta yi aiki kuwa. Hoton da aka baza na wadannan layuka, inda aka ware gefen masu tafiya, da na masu gudu a tsakiya da kuma na masu amfani da wayoyin hannu a daya gefen, ya janyo hankula sosai a kafofin sada zumunci na Intanet a wannan watan.

Duk da cewa an ware wurin bin masu amfani da wayoyin hannun a matakalar da ta shiga zuwa dakin motsa jiki da wuraren shakatawa na jami'ar ne kawai, wata daliba mai suna Tasia Briggs, 'yar shekaru 22 da haihuwa, ta ce zata so ta ga an kara yawansu cikin harabar jami'ar.

Ta ce, "akwai haushi kana tafiya a bayan mutum yana ta rubutun wani abu a wayarsa, yana bata maka lokaci don duk hankalinsa na kan wayar."

Jami'ar Utah Valley tana garin Orem, mai tazarar mil 40 daga Salt Lake City, babban birnin jihar. Jami'ar tana da dalibai dubu 31.

XS
SM
MD
LG