Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Cikin Damuwa da Firgici


Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha
Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha

Halin da tattalin arzikin Najeriya, ke ciki yasa talakawa da shuwagabani suna kokawa shugaban kungiyar Gwamnonin APC, kuma Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, yace “muna cikin damuwa da firgici bisa yadda kudaden shigar jihohi ke samun koma baya da a yau ya kawo nakaso ga rayuwar jama’ar, mu.

Dole ne a dauki matakan gaggawa domin ‘yantar da jihohi, muna kiran a yiwa tsarin tattalin arziki gyaran fuska dan lillike wuraren dake yoyo a baitulmalin Najeriya, rashin iya gudanar da tattalin arzikin kasar na ne ya kai kasar ga wannan hali na ni ‘yasu, a gaskiya ma dai Gwamnatin APC ta samu baitulmalin kasar kusan fayau.

Halin dai da tattalin arzikin Najeriya, ke ciki a halin yanzu har ta kai ga jihohi goma sha takwas basu iya biyan albashi, doba da yadda ake ta yama didi bisa kan kudaden da Gwamnati ke kashewa masamman akan ‘yan majalisu, wani tsohon dan majalisar Dr.Almajiri Gyadam, ya na mai cewa yakamata mu tashi gabadaya mu ceci wannan kasar babu kudin shiga kamar yadda aka saba, ‘yan majalisa ba sai wai bangaren Gwamnati sun ce sun yanke albashin su kuma su nemi ‘yan majalisa ma suyi haka ba majalisa yakamata suyi jagorancin taimakawa kasa su rarrage duk wasu abubuwa da suke ganin mutanen kasar nan basu jin dadi akansu kuma su kansu sun san cewa abubuwa ne da basu kan hanya.

XS
SM
MD
LG