Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Mutun-Mutumi Na Rayuwa Kamar Kowa


Masana na cigaba da zurfafa bincike wajen maida mutun-mutumi “Robot” tamkar mutun, shahararren kanfanin kera robot na kasar China, sun kirkiri wani sabon mutun-mutumi da suka sama suna “Nxrob”, da yake mu’amala da mutane kamar yadda mutane suke gabatar da zaman takewar su a tsakanin jinsin dan’adam.

Shidai sabon mutun-mutumin yakan gabatar da duk wasu abubuwa da mutun kanyi a gida, kunna talabijin, kunna na’urar dimama daki, da sanin irin yanayin da ya kamata mutun ya zauna a cikin daki, yana fira da mutun don bashi labarin dariya da abubuwan ban mamaki.

Haka mutun mutumin, yakan yi wasa da yara, da tuna musu wasu abubuwa da ya kamata ace sunyi a kowane lokaci a rana, yakan tinama yaro cewar an bashi aikin gida daga makaranta, don haka sai ya kokarta wajenyi.

Bai tsaya nan kawai ba, yakan san kowane mutun da yake a cikin gida, da irin abun da kowane mahaluki yake bukata, kamar irin kalan kayan da mutun yake so da irin abincin da mutun yafi so. Haka idan dakin mutun yayi sanyi ko zafi bayan mutun na bacci, roboto din yakan sauya yanayin dakin wajen kunna na’urar da zata maida dakin wajen zama batare da damuwa ga lafiya mutun ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG