Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ronaldo Ya Ci Kwallayensa Na Farko a Juventus


Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo

Magoya bayan kungiyar ta Juventus sun barke da sowa da nuna farin ciki a lokacin da Ronaldo mai shekaru 33 ya saka kwallon farko jim kadan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronald ya ci kwallayensa na farko a sabon Club dinsa na Juventus da ke Italiya.

Ya ci kwallaye biyu ne a wasan da suka kara da Sassualo inda aka tashi da ci 2-1.

Ronaldo ya yi fama da farin kwallaye tun bayan da ya koma kungiyar ta Juventus a wasanninta uku da ta buga a baya.

Kwallon farko ta zo ne jim kadan bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Sannan ya zura ta biyu cikin minti na 65 yayin da dan wasan Sassualo Khouma Babacar ya farke guda.

Magoya bayan kungiyar ta Juventus sun barke da sowa da nuna farin ciki a lokacin da Ronaldo mai shekaru 33 ya saka kwallon farko.

Shi dai Ronaldo dan asalin kasar Portugal, ba bakon cin kwallaye ba ne, amma ya gaza cin kwallo ko daya tun da aka fara gasar ta Serie A a wasanni da Juventus ta buga a baya.

Dan wasan ya jima yana dakon kwallonsa ta farko, lamarin da ya sa har masu sharhi ke cewa ya shiga yanayi na kunci.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG