Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gareth Southgate Ya Ce Zai Ba Harry Kane Hutu


Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila Gareth Southgate ya ce zai ba dan wasan gabansa Harry Kane hutu a wasan sada zumunta da Ingila zata yi tsakanita da kasar Switzerland, a ranar talata 11/9/2018.

Kane wanda yake taka leda a kungiyar Tottenham mai shekaru 25 da haihuwa, ya samu nasarar zurara kwallaye shida, a gasar cin kofin duniya inda ya lashe lambar zinare na dan wasan da yafi zurara kwallaye a gasar cin kofin duniya 2018 wanda ya gudana a Rasha.

Haka kuma a lokacin rani, ya fafata wasanni 61 a duk wasannin tun farkon kakar wasa ta shekarar data gabata. Sai dai abokin wasan Kane a Tottenham Dele Alli, baya cikin tawagar sakamakon wani rauni a tsokar kafarsa (muscle strain) da yake fama dashi.

Dan wasan baya na Manchester United, Luka Shaw, ya bar sansanin a bayan da ya sha wahala a cikin wata mummunar haduwa da sukayi da Dani Carvajal, a wasan da suka yi da Spain a Wembley a ranar Asabar.

Sakamakon haka Gareth Southgate ya gayyato ‘yan wasa Ben Chilwell da kuma Demarai Gray, daga tawagar ‘yan kasa da shekaru 21 na kasar domin fafatawa a gasar ta ranar talata da Swiztland a Leicester's.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG