Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nishadi tare da Al-Amin Ibrahim


Nishadi tare da Al-Amin Ibrahim
Nishadi tare da Al-Amin Ibrahim

A shirinmu na nishadi a yau Mun Sami bakuncin mawaki Al-Amin Ibrahim wanda ya fara harkar waka tun yana dan yaro karami.

Ya ce tun yana firamare ya fara rubuce rubuce, ya kuma soma ne da wakar fim inda daga bisani ya fara wakokin harshen turanci da na Hausa.

Kawo yanzu kuma yana wakokin audio da ma na bidiyo, ya kuma sami award a wato lambar kyauta ta harkar wakokin sa a wata gasa da suka je jihar Niger.

Ya ce idan yana rere waka yana tsintar kansa cikin nishadi da jin dadin wanan arziki da Allah ya bashi na isar da sako ga alumma.

Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar da ma tseguminmu na yau.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG