Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kendrick Lamar Ne Kan Gaba Cikin 'Yan Takarar Karbar Lambobin Yabo Na Grammy Na 2016


Yayinda ake shirye-shiryen bukin Grammy na shekarar 2016 wanda ake yi a Amurka duk shekara, shahararren mawakin nan mai suna Kendrick Lamar ya sami wani babban albishir.

Sunan Kendrick Lamar ya sami shiga cikin jerin wadanda za su yi takarar karbar lambobin Grammy a rukunoni har goma sha daya, kusan sunansa ne ya fi yawa cikin masu neman Kambin na shekarar 2016, bukin da za a yi ranar 15 ga watan Fabairu in Allah Ya kaimu. Wakokinsa masu tashe sun hada da “To Pimp a Butterfly” da kuma “Alright”.

Duk da kokari da kuma sunan da wakokin wasu mawakan suka yi a shekarar nan ta 2015, sunan su bai shiga takarar ba ko sau daya.

Mai bin bayansa kuma ita ce mawakiya Taylor Swift, wadda sunanta ya fito sau 7 cikin ‘yan takarar. Wakokinta da suka yi tashe sun hada da “Butterfly” da kuma “Beauty Behind Madness”.

XS
SM
MD
LG