Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nishadi Tare Da Usman S Aliyu


Usman Aliyu Mawaki
Usman Aliyu Mawaki

A shirinmu na nishadi a yau muna tare da Usman S Aliyu wani makadin mawaka , kamar dai yadda masu iya magana kan ce yau da gobe ya fi gaban wasa

Usman Aliyu ya ce yawan cudanya da yake yi da mawaka ya sa ya fara sha'awar waka har ta kai shi ga fara gwada rera wakar shekaru shida da suka wuce.

Yace ya fara da rubuta wakoki ne wasu na rerawa daga baya sai shima ya fara da kansa daga nan sai ya ajiye kida ya cigaba da rera wakoki.

Yana mai cewa har kullum burinsa shine ya duk wakar da zai yi ya kasance mai amfani ce ga aluma, kawo yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu.

XS
SM
MD
LG